(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Andry Rajoelina shugaban kasar ta Madagascar yana fadar haka a wani jawabinda ya yiwa mutanen kasar ta wata tashar talabijin ta gwamnatin kasar a jiya litini.
Shugaban ya kara da cewa banda wadanda suka mutu sanatoci a kalla 25 ne suka kamu da cutar a babban birnin kasar Antananaribo.
Tun watan Maris da ya gabata ne cutar ta korona ta bulla a kasar Madagascar, kuma ya zawa yanzu ta kama mutane 5,080 tare da mutuwar mutane 37 daga cikinsu.
Shugaban ya bayyana cewa ya na ci gaba shan magarin gargajiya na korona wanda majalisar dinkin duniya ta ce babu tabbacin yana maganin cutar.
342/